Cristiano Ronaldo na shirin zama gwarzon Duniya na 2017

Cristiano Ronaldo na shirin zama gwarzon Duniya na 2017

- FIFA ta fitar da ‘Yan wasan da za su lashe kyautar Ballon D’or

- Daga ciki dai Dan wasa Cristiano Ronaldo ne a kan gaba bana

- Babban ‘Dan wasan ne ya lashe wannan kyautar a shekarar bara

Ku na da labari cewa Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kawo jerin ‘yan wasan da a cikin su za a zabi gwarzon wannan shekarar.

Cristiano Ronaldo na shirin zama gwarzon Duniya na 2017

Dan wasa Ronaldo zai kamo Lionel Messi?

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ne ake sa rai zai zama gwarzon Duniya a bana kamar dai abin da ya faru a bara. Wannan shekarar ma ‘Dan wasan ya dauki Kofin UEFA Champions League na Turai da Kofin La-Liga na gida da wasu Kofunan.

KU KARANTA: Hukumar ta FIFA ta zakulo manyan ‘Yan wasa 15 na 2017

Bayen Kofunan da ‘Dan wasan ya samu haka kuma ya jefa kwallaye barkatai musamman a Gasar Nahiyar Turai. Idan Dan kwallon ya zama gwarzon Duniya zai zama kenan ya kamo kafar Lionel Messi na Barcelona wanda ya taba daukar kofin sau 5 a Duniya.

Hukumar ta FIFA ta zakulo ‘Yan wasan da ake sa rai za su lashe kyautar kuma manyan ‘Yan wasan Duniya irin su Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina da kuma Gianluigi Buffon ne a kan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel