Zan saye Arsenal kuma in kori Koci Arsene Wenger Inji Dangote

Zan saye Arsenal kuma in kori Koci Arsene Wenger Inji Dangote

- Aliko Dangote ya kara jadadda cewa yana da niyyar sayen Arsenal

- Attajirin ya ce yana sayen Kungiyar kwallon kafar zai kori Wenger

- Dangote ya dade yana da muradin ganin ya saye Arsenal nan gaba

Mai kudin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya kara jadadda cewa yana nan da niyyar sa na sayen Kungiyar Arsenal nan gaba.

Zan saye Arsenal kuma in kori Koci Arsene Wenger Inji Dangote

Dangote yana nan a kan bakar sa na sayen Arsenal nan gaba

A wata hira da Mai kudin Duniyar yayi da Jaridar Finacial Times ta barin Afrika, Dangote ya jaddada muradin sa na sayen Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Dan kasuwar yace akwai wasu ayyuka da ya sa gaba wanda su ka hana sa sayen Kungiyar a yanzu.

KU KARANTA: Me yasa Dangote ke sha'awar sayen Arsenal?

Aliko Dangote ya bayyana cewa da zarar ya sayen Kungiyar zai kuma fatattaki wasu mutanen ciki. Dangote dai yace tuni zai yi waje da irin su Kocin Kungiyar Arsene Wenger. Dangote yayi magana game da yanayin aiki a Afrika.

Attajirin Afrika ya dade yana goyon bayan Kungiyar kwallon kafar kuma ya saba cewa zai kori Kocin Kungiyar saboda rashin cin kofi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel