Za a gwabza wajen neman Shugabancin Jam'iyyar PDP

Za a gwabza wajen neman Shugabancin Jam'iyyar PDP

- Gbenga Daniel yace ba zai janye takarar Shugabancin PDP ba

- Tsohon Gwamnan yace babu wanda zai sauka ya marawa baya

- Ana kishin-kishin din zai hakura ya bar wa Bode George takarar

Bisa dukkan alamu dai za a gwabza wajen neman Shugabancin Jam'iyyar PDP mai adawa a Kasar nan inda tsohon Gwamnan Jihar Ogun Gbenga Daniel yace babu ja da baya

Za a gwabza wajen neman Shugabancin Jam'iyyar PDP

Gbenga Daniel yana neman Shugabancin PDP

Mun samu labari daga Jaridun Kasar nan cewa Dan takarar Shugabancin Jam'iyyar PDP Gbenga Daniel ya bayyana cewa yana nan a kan bakar sa na tsayawa takarar Jam'iyyar. Daniel yake cewa ba zai hakura ya janyewa kowa ba.

KU KARANTA:

Akwai dai rade-radin cewa Gbenga Daniel zai hakura ya bar wa George takarar amma yace babu wannan maganar don kuwa shi ya fi dacewa sa kujerar. Gbenga Daniel yace wasu na neman kujerar ne domin abin da za su samu.

Akwai dai sauran 'Yan takara da dama da ke neman kujerar sai dai tsohon Gwamnan Daniel yace ya fi kowa cancanta. Ciki har da wasu tsohofaffin Ministoci ilmi na kasar Farfesa Taoheed Adedoja da Farfesa Tunde Adeniran.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel