Rikicin Baru da Kachikwu: Kungiyoyin ma'aikatan man fetur sun goyi bayan Baru

Rikicin Baru da Kachikwu: Kungiyoyin ma'aikatan man fetur sun goyi bayan Baru

- Kungiyoyin albarkatun man fetur sun yi mubaya'a ga Maikanti Baru game da sabanin da ya samu da Karamin Ministan Mai wato Ibe Kachikwu

- Sun ce sukan da Kachikwu ya yi wa Baru ba gaskiya bane

- Kungiyoyin sun yi kira ga 'yan Najeriya da su iya bakunan su game da sabanin

A ranar Litini ne Kungiyoyi guda 2 na albarkatun man fetur su ka goyi bayan Babban Manaja na Ma'aikatar Matatan Man Fetur na Kasa (NNPC) wato Maikanti Baru a game da sabanin da ke tsakaninsa da Karamin Ministan Man Fetur Ibe Kachikwu.

Wadannan Kungiyoyin su ne: Kungiyar Manyan Ma'aikata na Albarkatun Man Fetur na Kasa wato PENGASSAN da kuma Kungiyar Ma'aikata na Albarkatun Man Fetur na Kasa wato NUPENG.

Rikicin Baru da Kachikwu: Kungiyoyin ma'aikatan man fetur sun goyi bayan Baru

Rikicin Baru da Kachikwu: Kungiyoyin ma'aikatan man fetur sun goyi bayan Baru

Mista Ndu Ughamadu wanda Karamin Manaja ne a NNPC shi ne ya bayar da sanarwan wannan mubaya'a a Abuja. A cewar sa, Mista Baru ya yi komai bisa ka'ida da bin doka sabanin zargin da Dakta Kachikwu ya yi masa.

DUBA WANNAN: Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

A jawabin mubaya'a da suka gabatarwa Baru lokacin da suka kai masa ziyara, sun ce suna goyon bayan sa ne saboda aiki tukuru da yake yi tun hawar sa kujerar Babban Manaja.

A cewar su Baru ya kawo daidaito a NNPC kuma sakamakon jajircewansa kan aikin sa ne ya kai ga zama Babban Manaja. Sun ce zasu cigaba da yi masa addu'ar menan kariya da daukaka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel