Makurdi: Gwamnati na ta kasa cika alhakin biyan albashin ma’aikata – Inji gwamna Ortom

Makurdi: Gwamnati na ta kasa cika alhakin biyan albashin ma’aikata – Inji gwamna Ortom

- Gwamnatin jihar Binuwai ta ce ta kasa cika alhakin biyan albashin ma'aikatan jihar

- Gwamnan ya gana da shugabannin kungiyar kwadago a ranar Litinin a Makurdi

- Ortom ya ce rashin iya biya albashin ma’aikata ta wuce karfin gwamnatinsa

Gwamna na jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya amince cewa gwamnatinsa ta kasa cika alhakin biyan albashin ma'aikatan jihar.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, gwamnan ya amince da wannan batu a Markudi babban birnin jihar bayan ganawa da shugabannin kungiyar kwadago a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.

"Ma'aikaci sun cancanci albashin su, amma gwamnatin Binuwai ba ta iya cika wannan alhaki ba. Mun gaza ga ma'aikata a wannan batun", in ji Ortom a Makurdi.

Makurdi: Gwamnati na ta kasa cika alhakin biyan albashin ma’aikatan Binuwai – Inji gwamna Ortom

Gwamna na jihar Binuwai, Samuel Ortom

Ya ce abubuwan da ke da alhakin rashin iya biya albashin ma’aikata ta wuce karfin gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Yan jam’iyyar APC da na GPN 4,500 sun canza sheka zuwa jam’iyyar NNPP a Bauchi

"Gwamnatin ta damu da rashin iya biya ma'aikata kuma ta kafa kwamitin hadin gwiwar, wanda ya haɗa da ma'aikatun gwamnati da jami'an gwamnati, don bincika batutuwan da ke kewaye da rashin iya biya albashi”.

"Kwamitin za ta kuma duba cikin al'amarin yadda za a rage kudaden albashin jihar na naira miliyan 7.8", inji shi.

Wabba da Ortom, duk da haka, sun ki bayyana matakan gwamnati a kan abin da za ta bayar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel