Agbakoba ya kai gwamnatin Buhari a gaban kotu akan ‘yan kabilar Igbo

Agbakoba ya kai gwamnatin Buhari a gaban kotu akan ‘yan kabilar Igbo

- Tsohon shugaban kungiyar NBA ya kai karan gwamnatin tarayya a kan rashin adalci ga yankin kudu maso gabas

- Agbakoba ya ce nade-naden da aka a kamfanin NNPC a watan Agustan da ta gabata ta saba wa tsarin mulkin kasar

- Babban lauyan ya ce tsarin mulkin Najeriya ta haramta nuna bambanci ga dukkanin kabilanci na Najeriya har da ‘yan kabilar Igbo

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Olisa Agbakoba (SAN) ya gabatar da kara a gaban babban kotun tarayya da ke birnin Abuja, yana kalubalantar gwamnatin tarayya a kan rashin shigar da yankin kudu maso gabashin Najeriya a cikin sabbin nade-naden da aka yi a kamfanin NNPC a kwanukan baya.

Agbakoba a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba ya yi zargin cewa nadin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi, ya saba wa ka'idodi na S.14 na kundin tsarin mulki da kuma dokar yankin tarayya da kuma tanadi na sashe na 42 na tsarin mulkin Najeriya wanda ya haramta nuna bambanci ga dukkanin kabilanci na Najeriya kamar su, a wannan batu, kudu maso gabas.

Tsohon shugaban ya bukaci babban kotun ta bayyana wannan nadin da NNPC ta yi ba tare da sun hada da kowane mutum daga yankin kudu maso gabas ba a matsayin saba wa tsarin mulki kuma wanda bai dace ba.

Agbakoba ya gurfanar da gwamnatin Buhari a gaban kotu akan ‘yan kabilar Igbo

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Olisa Agbakoba (SAN)

Har yanzu babban kotun ba ta sanya ranar sauraron wannan kara ba.

KU KARANTA: Karya minista Ibe Kachikwu yayi mani - Maikanti Baru

Idan baku manta ba, NAIJ.com ta ruwaito a watan Agustan da ta gabata cewa kimani ma'aikatan kula da albarkatun man fetur na Najeriya, NNPC 55 aka dakatar a cikin wani shirin da babban darakta NNPC Maikanti Baru ya umarta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel