Arewa za ta yi matsaya a kan sake fasalin Najeriya ranar Laraba

Arewa za ta yi matsaya a kan sake fasalin Najeriya ranar Laraba

- Yankin arewacin Najeriya za ta bayyana matsayin ta a shirin sake fasalin kudi tsarin kasar

- ARDP ta ce za ta shirya taron kwana biyu a Kaduna a ranar Laraba don tattaunawa a batun

- Taron za ta ba al’umma damar ba da nasu gudunmawa a tattaunawa

Shugaban cibiyar bincike da bunkasa yankin arewa, ARDP, Usman Bugaje, ya ce arewacin Najeriya za ta yi matsayi a kan sake fasalin kudi mulkin kasar bisa ga bincike da kuma amincewa maimakon na tausin zuciya da son kai.

Bisa ga wannan batu, ARDP ta ce za ta shirya taron kwana biyu a Kaduna a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba.

NAIJ.com ta tattaro cewa, Bugaje ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka bayar a birnin Abuja a ranar Lahadi. Tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa kuma tsohon dan majalisar wakilai ya ce ya zama wajibi ga arewa ta gabatar da matsayin ta a wannan batu.

Arewa za ta yi matsaya a kan sake fasalin Najeriya ranar Laraba

Shugaban cibiyar bincike da bunkasa yankin arewa, ARDP, Usman Bugaje

Bugaje ya ce, "A cikin shekara daya da ta gabata, sake tsarin mulkin kasar da kuma tarayyar ta gaskiya ta mamaye jawabai na siyasa a Najeriya. Abin takaici, idan kun saurari jawabai da kuma karanta labari a kan waɗannan batutuwa, za ku ga cewa akwai fahimtar waɗannan kalmomi daban-daban kamar yadda mutane suke magana ko rubuta”.

KU KARANTA: Za a gwabza wajen neman Shugabancin Jam'iyyar PDP

Yayin da yake jawabi a kan taron, Bugaje ya ce, "Wannan taro za ta hada da malaman makarantu tare da siyasa na gaskiya, yayin da masana zasu gabatar da takardu a kan shirin, kuma za a yi zaman tattauna batun”.

"Za a kuma ba masu sauraron damar ba da nasu gudunmawa a tattaunawa”, inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel