Tinubu ya tsara abubuwa 7 wanda zai iya farfado da tattalin arzikin Najeriya

Tinubu ya tsara abubuwa 7 wanda zai iya farfado da tattalin arzikin Najeriya

- Tsohon gwamnan jihar Legas, sanata Bola Tinubu ya tsara abubuwa 7 wanda zai iya farfado da tattalin arzikin kasar

- Tinubu ya ce matakan 7 zasu rage yawan dogaro a kan albarkatun man fetur

- Tsohon gwamnan ya ce fadowar farashin man fetur a duniya ya nuna tsarin tattalin arzikin Najeriya

Jagoran shugaban jam'iyyar mai mulki, APC, sanata Bola Tinubu, ya ba da shawara a kan abubuwa 7 da za ta farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, babban jami'in APC, ya ce, matakan zasu rage yawan dogaro a kan albarkatun man fetur.

A cewar Tinubu, ci gaba da shirin gina kasa da sake dawo da hukumomin musayar kayayyaki da kuma gabatar da shirye-shiryen gidaje masu goyon baya na gwamnati, wadannan ne matakan da zasu taimaka wajen mayar da tattalin arzikin kasa.

Tinubu ya tsara abubuwa 7 wanda zai iya farfado da tattalin arzikin Najeriya

Jagoran shugaban jam'iyyar mai mulki, APC, sanata Bola Tinubu

Jerin abubuwan da tsohon gwamnan jihar Legas ya bayar sun hada da:

1. Mayar da hankali kan shirin gina kasa yana da amfani mai mahimmanci

2. Shawo kan tattalin arziki da siyasa da kuma tsarin mulki wanda ya hana kasar samun wutar lantarki mai daurewa

3. Samar da kayan bashi mafi sauki ga mutane masu matsakaici

4. Samar da jinginar gida na dogon lokaci

5. Sake dawo da hukumomin musayar kayayyaki, wanda zai ba manoma damar samun kyawawan farashi

6. Kaddamar da kamfanonin da za su tallafa wa aikin noma

7. Mayar da hankali ga masana'antu don samar da kayayyaki da 'yan Najeriya da sauran ƙasashen duniya suke son su saya

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

Wadannan abubuwan da aka tsara sun kasance wani ɓangare na jawabin da Tinubu ya gabatar a kwanan nan a Legas, inda ya ce fadowar farashin man fetur a duniya ya nuna tsarin tattalin arziki na kasar.

Tinubu ya ce wadannan manufofin na daga cikin abin da gwamnati za ta iya aiwatar. Ya ci gaba da cewa mayar da hankali kan waɗannan da sauran irin waɗannan abubuwa ya isa gwamnatin tarayya aiki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel