Kwallon kafa: FIFA ta fitar da gwaraza 15 na shekarar 2017

Kwallon kafa: FIFA ta fitar da gwaraza 15 na shekarar 2017

- FIFA ta kawo ‘Yan wasan da za su iya lashe kyautar Ballon D’or

- Hukumar kwallon kafar ta kawo jerin ‘Yan wasa 15 Duniya

- Daga ciki dai irin su Dan wasa Cristiano Ronaldo ne a kan gaba

Za ku ji cewa Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kawo jerin ‘yan wasa 15 wanda a cikin su za a fitar da gwarzon wannan shekarar.

Kwallon kafa: FIFA ta fitar da gwaraza 15 na shekarar 2017

Ronaldo na cikin gwarazan 'Yan wasan Duniya na bana

Hukumar ta FIFA ta zakulo ‘Yan wasan ne daga jerin da ta fitar kwanaki na ‘Yan wasa 30 a Duniya. ‘Yan wasan sun hada da ‘Yan kwallon Real Madrid, Barcelona, Tottenham, Chelsea, Roma, Manchester United da Manchester City.

KU KARANTA: Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta a wasan Zambia

‘Yan wasan sun hada dai da:

1. Patrick Aubameyang

2. Karim Benzema

3. Edison Cavani

4. Leo Bonucci

5. Gianluigi Buffon

6. Falcao

7. Antoine Griezman

8. Eden Hazard

9. Matts Hummels

10. Isco

11. Toni Kroos

12. Sadio Mane

13. Kylian Mbappe

14. Lionel Messi

15. Cristiano Ronaldo

Ku na da labari cewa manyan ‘Yan wasan Duniya irin su Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina ma dai su na cikin rudu domin har yanzu kasashen su ba su kai labari ba a Gasar World Cup tukuna.

Za a kawo sunayen irin su Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, Antoine Griezman, kuma Gianluigi Buffon daga baya kamar yadda mu ka samu labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel