Cutar Monkey Pox na cigaba da barkewa a Najeriya

Cutar Monkey Pox na cigaba da barkewa a Najeriya

- Cutar ‘Monkey Pox’ na cigaba da shiga Garuruwa

- An samu Jihohi 6 da cutar ta kwankwasa masu a yanzu

- Har yanzu wannan cuta ba ta da magani a Duniya

Kwanaki ku ke jin labari cewa wata sabuwar cuta da ake kira da Turanci ‘Monkey Pox’ mara magani ta barke a Najeriya.

Cutar Monkey Pox na cigaba da barkewa a Najeriya

Annobar Cutar Monkey Pox na kara tsanani

A halin yanzu wannan cuta ta shiga wasu sababbin Jihohi 6 kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto dazu. Yanzu haka cutar ta ratsa Jihar Ogun, Legas, Ekiti, Akwa-Ibom, Ribas, Bayelsa da kuma Jihar Kuros-Riba da ke Kudancin Kasar.

KU KARANTA: Za a kori Malamai 20,000 daga aiki a Kaduna

Da farko dai cutar ta fara yaduwa ne a Jihar Bayelsa amma yanzu da alama abin ya shiga wasu wurare kamar yadda bincike ya nuna. Akwai dai mutane 31 da ke fama da cutar yanzu a Najeriya wanda ake kula da su a asibiti.

Wannan cuta dai na sa kuraje su fesowa mutum a jiki. Kuma cutar ba ta da magani sai dai ayi ta kokarin rigakafi domin gudun daukar wannan cutar daga mutum ko dabbobin daji. Asali dai daga biri aka fara samun wannan cuta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel