Evans na shirya makircin tserewa tare da hadin baki wasu 'yan sanda

Evans na shirya makircin tserewa tare da hadin baki wasu 'yan sanda

- Jami’an tsaro sun gano Evans na shirya makircin tserewa tare da hadin baki wasu jami'an 'yan sanda daga gidan yari

- Ana zargin Evans da ba da cin hanci tsakanin dala 50,000 da 100,000 ga daya daga cikin masu tsaron sa

- ‘Yan sanda sun gano Evan na samun wayoyi daga mambobin kungiyarsa

Rahoton da jaridar The Nation ta bayar ya nuna cewa fitacce mai garkuwa da mutane Evans ya yi niyyar tserewa daga 'yan sanda kafin gurfanar da shi gaban kotu a kwanan nan.

A cewar rahoton, 'yan sanda, musamman ma wadanda ke sashin hikima, sun sami nasarar a kan dakatar da makircin tserewar.

A sakamakon haka, hukumar NPS ta kafa tsaro mai tsanani a kan wanda ake zargi da sace mutane.

Evans na shirya makircin tserewa tare da wasu jami’an 'yan sanda

Mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka sani da Evan

Wani majiya da aka nakalto a cikin rahoton, ya ce Evans ya shirya ya ba da cin hanci tsakanin dala 50,000 da 100,000 ga daya daga cikin masu tsaro da ke kula da inda ya ke don yunkurin tserewa.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun kama wani mutumi dauke da makami a gidan Kanu

Majiyar NAIJ.com ta ce an yi zargin cewa, Evans yana shirya yadda zai tsere tare da wasu mambobin ƙungiyarsa ta hanyar tarho.

An bayyana cewa jami'an tsaro sun gano makircinsa a cikin sauri.

"Lokacin da Evans yake hannunmu, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya tsere, amma mun ci nasara akan makircinsa. Mun gano cewa yana samun wayoyin da aka boye a tsakiyar burodi da tuwon garin kwaki da kuma sauransu", inji su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel