LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kaduna za ta dakatar da malaman makarantun firamare 20,000

LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kaduna za ta dakatar da malaman makarantun firamare 20,000

- Gwamanatin jihar Kaduna ta ce za ta dakatar da wasu malamai 20,000 a jihar

- An yi zargin cewa fiye da malaman makarantun firamare 20,000 sun kasa cin nasara a jarrabawar aji 4 na firamare

- Gwamna El-Rufai ya ce za a dauki wasu sabbin malamai akalla 25,000 a jihar

Gwamanatin jihar Kaduna ta bayyana cewa akalla malaman 20,000 ne za a dakatar a jihar bayan da suka fadi warwas a wani gwajin jarrabawa da aka shirya.

Fiye da malaman makarantun firamare 20,000 ne sun kasa cin nasara a jarrabawar aji 4 na firamare a jihar Kaduna bayyan wani yunkurin tacce malaman.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa za a dakatar da malaman sannan kuma a dauki wasu sabbin akalla 25,000.

LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kaduna za ta dakatar malaman makarantun firamare 20,000

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai

Gwamnan ya ce: “Mun san cewa mutane za su soki wannan yunkurin, amma muna da tabbacin cewa abu ne da ya kamata muyi kamar yadda ilimin 'ya'yanmu ya yi mahimmanci kuma bai daice a yi siyasa da hakan ba”.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da wasu Gwamnonin Arewa a fadar Shugaban kasa

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel