Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

Labaran kishin-kishin din da muke samu daga majiyoyi da dama sun nuna cewa wakillan shahararren dan siyasar nan, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam'iyya mai mulki Alhaji Atiku Abubakar sun fara wata ganawar sirri da wakillan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Haka ma dai labaran da dada kara nuni da cewa dan siyasar da yayi takarar tikitin shugaban kasa a jam'iyyar APC a shekara ta 2015 yana daf da ficewa ya bar jam'iyyar ya koma jam'iyyar sa ta asali watau PDP.

Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

KU KARANTA: Yadda Sanata Ben Bruce da wata kungiya suka kwashi yan kallo

NAIJ.com ta samu dai cewa tuni dai dama danganta tsakanin Atiku Abubakar din da shugaba Jonathan ta soma sake kankama inda aka ruwaito cewar Jonathan din ya shawarci Atiku da ya gaggauta komawa jam'iyyar ta PDP da wuri domin samun damar tsayawa takarar.

Ma su fashin baki da dama dai na ganin cewa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 sai tafi yiwa Atiku saukin samu a jam'iyyar PDP bisa ga jam'iyyar APC mai mulki duba da yiwuwar cewar jam'iyyar zata fi ba shugaba Buhari muhimmanci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi

NAIJ.com
Mailfire view pixel