Garabasa: Jam'iyyar PDP ta baiwa mata masu son takara fom kyauta

Garabasa: Jam'iyyar PDP ta baiwa mata masu son takara fom kyauta

- Mata za su kwashi garabasa a jihar Delta ta kudu-maso-kudancin Najeriya

- Matan a jihar za a raba masu fom din takarar zabukan kananan hukumomin jihar kyauta

- Jam'iyyar PDP ta ce tayi hakan ne domin ta karfafawa mata gwuiwa

Jam'iyyar PDP a jihar Delta ta ayyana bawa mata masu son shiga a fafata dasu a zaben kananan hukumomin mai zuwa a shekara ta 2018 fom din takarar kyauta.

Jam'iyyar ta ayyana cewa bayar da fom din kyauta anyi shi ne dai da nufin karfafawa matan gwuiwa domin su fito a rika damawa da su.

Garabasa: Jam'iyyar PDP ta baiwa mata masu son takara fom kyauta

Garabasa: Jam'iyyar PDP ta baiwa mata masu son takara fom kyauta

KU KARANTA: Shugaban jami'an yan sanda yafi karfin mu - Hukumar gudanarwa

NAIJ.com ta samu dai cewa sauran yan takarar maza kuwa za'a saida masu fom din takarar shugaban karamar hukuma a kan Naira miliyan daya sai kuma Naira 200,000 kuma na kansila.

Haka nan kuma shugaban jam'iyyar na jihar masi Kingsley Esisco ya bayyana cewa tuni ma kuma jam'iyyar ta umurci sauran mukarraban jam'iyya a kananan hukumomin jihar da su kebe akalla fom din kansiloli uku domin mata zalla a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel