Karya minista Ibe Kachikwu yayi mani - Maikanti Baru

Karya minista Ibe Kachikwu yayi mani - Maikanti Baru

Shugaban rukunin kamfanonin mai na NNPC, Maikanti Baru, a cikin wata sabuwar sanarwar manema labarai ya musanta zargin aikata laifi wajen bayar da kwangiloli da karamin ministan mai Dakta Ibe Kachikwu ya yi masa.

Wannan jawabin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar ta NNPC mai suna Ndu Ughamadu inda yace zargin da aka yi wa shugaban kamfanin ya bayar da kwangilar da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 15 karya ce tuburan.

Karya minista Ibe Kachikwu yayi mani - Maikanti Baru

Karya minista Ibe Kachikwu yayi mani - Maikanti Baru

KU KARANTA: Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari - Dakta Gamawa

NAIJ.com dai ta kuma samu cewa Ndu Ughamadu ya labarta cewa kamfanin ya bi dukkan matakan da doka ta shimfida masa da kuma dukkan ka'idojin da suka dace wajen bayar da kwangilolin.

Haka kuma duk dai a cikin sanarwar da aka rarrabawa manema labarai, ya kuma bayyana cewa doka bata kayyade kudaden kwangilolin da kamfanin zai iya badawa ba, saboda suna matakin yarjeniyoyi ne, haka kuma a karkashin doka kamfanin ba ya bukatar tattaunawa ko sake duba kwangiloli daga wajen ministan.

Mai karatu dai zai iya sanin cewa a karshen watan Agustan da ya wuce ne karamin ministan mai na Najeriya ya rubuta wa shugaban kasa kuma babban ministan mai wata wasika yana mai zargin shugaban kamfanin na NNPC da rashin bin ka'idoji wajen bayar da manyan kwangolili, da kuma rashin yi masa biyayya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel