Nnamdi Kanu ya yi amfani da jinyar mijina wajen cin karensa ba babbaka - Aisha Buhari

Nnamdi Kanu ya yi amfani da jinyar mijina wajen cin karensa ba babbaka - Aisha Buhari

- Aisha Buhari ta bayyana cewa Nnamdi Kanu da magoya bayansa sun rika cin karensa ba babbaka ne saboda sun ga cewa Buhari baya kasar

- Uwargidan shugaban kasar tace jinyar da Buhari ya yi a Ingila ya kawo tsaiko ga al'amurra da dama a Najeriya

Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa Shugaban Kungiyar masu fafutukar neman kafa yankin Biyafara ( IPOB), Nnamdi Kanu da magoya bayansa sun rika cin karensa ba babbaka ne saboda sun ga cewa maigidanta shugaba Muhammadu Buhari ba ya Najeriya yana can Ingila yana jinya.

Ta kara da cewa jinyar da Buhari ya yi a Ingila ya kawo tsaiko ga al'amurra da dama a Najeriya wanda ya ba Nnamdi Kanu damar neman magoya baya a bisa akidarsa ta neman kafa kasar Biyafara.

KU KARANTA KUMA: Buhari kamar cutar daji ne da ya kamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

Koda dai ba wai ta ambaci sunan Kanu kai tsaye bane, amma dai uwargidan Buhari tace wani dan shekaru 40 yayi amfani da rashin maigidan ta a kasar wajen kafa kasa cikin kasa.

Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na wata hukumar kula da lafiyar mata da yara, wanda aka gudanar a asibitin da ke cikin fadar shugaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel