Bincike ya nuna cewa akasarin ‘Yan ta’adda ba Musulmai bane

Bincike ya nuna cewa akasarin ‘Yan ta’adda ba Musulmai bane

– Ana yawan zargin Musulmai masu akida mai tsanani da kai hari a kasashen Duniya

– Sai dai bincike ya nuna cewa babu ruwan Musulunci da harin kamar yadda ake tunani

Mun samu wani rahoto cewa wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa akasarin ‘Yan ta’addan Duniya ba Musulmai bane.

Wani bincike da ya fito a Jaridar Independent ta kasar waje ta ce an gano cewa mafi yawan masu kai wa Jama’a hari a Kasar Amurka masu ra’ayin rikau ne kurum ba wai Musulmai ba. An dai dade ana sawa Musulmai da Musulunci ido wajen harkar ta’addanci a Duniya.

KU KARANTA: Ana zargin wani Mawaki da fyade a Amurka

A hararen da aka kai daga shekarar 2008 zuwa 2016 a Amurka an gano cewa mafi yawanci wasu ne masu ra’ayin bam-bam na siyasa ko kuma masu tsananin kishin fararen fata ne su ka kai ba masu tsananin ra’ayin Addinin musulunci ba.

Shugaban kasar Amurka na yanzu Donald Trump tuni dai ya hana wasu kasashen Duniya da yake zargi da ta’addanci shiga cikin Amurka. Sai dai ana samun hare-hare da dama daga ‘Yan kasar da kuma Jami’an tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel