Ana zargin wani babban Mawaki da aikata mugun laifi

Ana zargin wani babban Mawaki da aikata mugun laifi

– Ana zargin wani Mawaki da yi wa wata fyade a garejin mota

– Wata Mata ta kai karar Mawaki Nelly da laifin yin lalata da ita

– Ana tunani wannan mummunan abu ya faru ne a Ranar Asabar

An kai karar wani fitaccen Mawakin Duniya Kotu bisa zargin yi wa wata mata fyade a karshen makon da ta wuce.

Ana zargin wani babban Mawaki da aikata mugun laifi

Wata na karar Nelly yayi mata fyade

Ana zargin Babban Mawaki Nelly da yin lalata da wata mata a kan hanyar sa a mota zuwa wani dandali domin wasa. Shi dai Nelly tuni ya karyata wannan magana inda yace sharri ne kurum aka yi masa kuma gaskiya za tayi halin ta nan gaba kadan.

KU KARANTA: Mata na cikin matsala a Arewa Inji Rahma Sadau

Jami’ar ‘Yan Sanda na Unguwar da ake tunani abin ya faru sun kama Mawakin inda su ka garkeme sa da tsakar safiya. Sai dai mun fara samun labari cewa an sake Mawakin Cornell Haynes Jr bayan an gudanar da bincike a karshen makon da ta gabata.

Scott Rosenblum wanda shi ne Lauyan Mawakin ya bayyana cewa bayan dan lokaci kadan aka saki mawakin da ake zargi da aikata wannan abin assha! Lauyan dai yace sharri kurum ake yi wa Nelly.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel