Jami’an tsaro sun kama wani mutumi dauke da makami a gidan Kanu

Jami’an tsaro sun kama wani mutumi dauke da makami a gidan Kanu

Sojoji da yan sanda sun kuma kai mamaya gidan shugaban kungiyar masu fafutukar Biyafara, Nnamdi Kanu a Afaraukwu, Umuahia jiya a binciken makamai.

A ranar 14 ga watan Satumba, rundunar Operation Python Dance sun shiga gidan; tun bayan nan ba’a san inda Kanu yake ba.

Shugaban Operation Python Dance a jihar Abia yace “An kama wani da makami a haraban gidan”.

Jami’in rundunar soji, wanda yaso a bayyana shi a natsayin shugaban aikin, yace sun hada hannu ne da yan sanda. Yace masu kawo mana rahoto su tuntubi yan sanda don jin Karin bayani.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta caccaki ma’aikatan asibitin Aso Rock

Ya karyata ikirarin kanin Nnamdi Kanu, Emmanuel wanda ya zargi “mamayan sojin” sun dauke wasu abubuwa irin su talbiji, kayayyakin sawa da wasu abubuwa.

Jami’in yace sun kai mamayar ne bisa rahoto da suka samu na cewa sun boye a haraban gidansu.

Kakakin yan sandan jihar Abia Geoffrey Ogbonna bai dauki wayar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel