Wani babban Lauya ya kara kira Shugaba Buhari ya bar mukamin Minista

Wani babban Lauya ya kara kira Shugaba Buhari ya bar mukamin Minista

- Babban Lauyan Femi Falana ya ba Shugaba Buhari shawara

- Lauyan ya nemi Shugaba Buhari ya sauka daga matsayin Minista

- Shugaban Kasa Buhari ne babban Ministan man fetur na kasar

Wani babban Lauya a Kasar nan Femi Falana ya shawarci ya sauka daga matsayin sa na Ministan man fetur na Najeriya.

Wani babban Lauya ya kara kira Shugaba Buhari ya bar mukamin Minista

Falana ya nemi Shugaba Buhari ya sauka daga Minista

Femi Falana ya bayyana wannan ne saboda hatsaniyar da ke nema ya barke tsakanin karamin Ministan mai na kasar Ibe Kachikwu da kuma Shugaban Kamfanin mai na NNPC na kasar watau Dr. Maikanti Baru. Lauyan yace dole Shugaba Buhari yayi gyara a bangaren na fetur a Kasar.

KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa ta caccaki Diezani

Lauyan wanda ya saba magana game da harkokin kasar ya bayyana cewa abin da ya fi dacewa shi ne Shugaban kasar ya ajiye mukamin sa na Ministan ya ji da manyan ayyukan da ke gaban sa saboda lurarar rashin lafiya da Shugaba Buhari yake ta fama da ita tun ba yau ba.

Falana ya kuma kira Shugaban kasar ya binciki korafin da Ministan man fetur na kasar watau Dr. Kachikwu yake yi inda yace Shugaban NNPC ya kebe sa wajen daukar wasu matakai a Kasar. Falana yayi kira a dakatar da Shugaban na NNPC idan har yana da laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel