Aisha Buhari ta caccaki ma’aikatan asibitin Aso Rock

Aisha Buhari ta caccaki ma’aikatan asibitin Aso Rock

Aisha, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta caccaki ma’aikatan asibitin Aso Rock, inda ta zarge su da rashin amfani da kuma rashin aiki bayan kasafin kudi na biliyan 3.

A makon da ya gabata, Zahra Buhari ya je shafinta na Instagram ta caccaki sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, bisa rashin samar da koda maganin Paracetamol ne a asibitin duk da kasafin kudi na naira biliyan 3 da aka ware na asibiti.

Da yake magana a ranar Litinin a taron masu ruwa da tsaki na hukumar RMNCAH+N,a fadar shugaban kasa, Abuja, Aisha Buhari tace kwanaki tayi zazzabi aka bata shawarar zuwa Landan yin magani, amma ta ki.

“Na kira asibitin Aso don na tambaye su ko suna da mashin din X-Ry, sai suka ce baya aiki.

“Daga karshe dole naje wani asibiti mallakan yan kasar waje 100 bisa 100.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban hafsan soji, Victor Malu ya rasu

“Akwai kasafin kudi ga asibitin kuma idan kaje chan a yanzu, zaka ga ayyuka da dama dake gudana amma basu da koda sirinjin allura. Manene amfanin gine-ginen idan babu kayayyakin aiki?”

“kuyi tunanin mai zai faru ga matan gwamnoni a fadin jihohi idan hakan zai iya faruwa gare ni a Abuja,” inji ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel