Buhari kamar cutar daji ne da ya kamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

Buhari kamar cutar daji ne da ya kamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

- Fani Kayode ya ce duk sukar da yake yi wa gwamnatin Buhari gaskiya ne

- Tsohon ministan ya ce a shirye yake fuskanci kowani irin matsala dan kare mara sa karfi a Najeriya

- Femi ya kwatatnta shugaban kasa Muhammadu Buhari da cutar daji da yakamata a yanke shi

Tsohon ministar sufurin jirgin sama, Femi Fani Kayode ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da cutar “daji” wanda ya kamata a kawo karshen shi.

Fani-Kayode ya ce a shirye yake ya fuskanci ko wani irin matsala dan ceto yan Najeriya daga halin mulkin mallaka, zalunci, cin hanci da rashawa, kuncin rayuwa da banagarencin na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da yayi a shafin sa na Facebook, tsohon minitsar yace zai cigaba yin magana game da al’amuran da ya shafi wannan gwamnati.

Buhari kamar cutar daji ne da yakamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

Buhari kamar cutar daji ne da yakamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

Femi Fani-Kayode kuma jigo a jam’iyyar PDP, yace duk sukar da yake yi wa gwamnatin Buhari, gaskiya ne.

KU KARANTA : Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

“Wannan mutumin Buhari, kamar cutar da daji ne dake tsurowa a jikin dan Adam, maganin sa shine a yanke shi.

Wasu su ce irin adawar mu, zai iya sa rayuwar mu a cikin hatsari. Sun mata da cewa duk wanda ya dau hanyar fadar gaskiya dan kare mara sa karfi ya saka rayuwan sa cikin hatsari.

Tsohon ministar ya zargi Buhari da rufe albarkar Najeriya da duhun gwamnatin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel