Ba ni da niyyar tsayawa takara a 2019 — Osinbajo

Ba ni da niyyar tsayawa takara a 2019 — Osinbajo

- Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa bai da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019

- A cewar sa babu wannan tunanin a cikin tsarin shi

- Mataimakin shugaban kasar ya bayyana wadanda za su lashe zaben 2019 wanda yace ba shakka Jam'iyyar su ce ta APC

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa bai da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019, cewa kuma bai da lokacin yanke wannan shawara.

Jaridar Reuters ya rahoto cewa a wani jawabi da Osinbajo a taron kasashen Afirka wanda aka gudanar a Landan yace babu wannan tunanin a cikin tsarin shi.

Har yanzu dai al’ummar kasar na cikin duhu na rashin babbaci kan ko Shugaba Muhammadu Buhari yana da niyar sake tsayawa takara a 2019.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wadanda za su lashe zaben 2019 wanda yace ba shakka Jam'iyyar su ce ta APC.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ce ba abin da zai hana Jam'iyyar APC mai mulki nasara a zabe mai zuwa lokacin da yake amsa tambaya daga wani Dan Jaridar Channels TV. Osinbajo yace babbar matsalar kasar nan ita ce yaki da rashin gaskiya wanda ake kokarin tsaidawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel