Hadimar Shugaba Buhari tayi kaca-kaca da Diezani Alison-Madukwe

Hadimar Shugaba Buhari tayi kaca-kaca da Diezani Alison-Madukwe

- Wata Hadimar Shugaban kasa Buhari ta caccaki tsohuwar Ministar mai

- Lauretta Onochie tace tsohuwar Ministar Alison-Madukwe ba ta gaskiya

- Ana tuhumar Ministar Jonathan da amfani da matsayin ta a Gwamnati

Mun samu labari cewa wata Hadimar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tayi kaca-kaca da tsohuwar Minista Diezani Alison-Madukwe.

Hadimar Shugaba Buhari tayi kaca-kaca da Diezani Alison-Madukwe

Mai ba Shugaba Buhari shawara ta soki Diezani

Lauretta Onochie tayi rubutu a shafin ta na Facebook game da tsohuwar Ministar da ke kokarin dawowa Najeriya domin shari'ar ta. A cewar ta Diezani ta tsere ne zuwa Kasar Birtaniya da sunan rashin lafiya da niyyar ta sulale zuwa kasashen ketare domin ta tserewa Hukuma.

KU KARANTA: Atiku yayi magana game da harkar zabe

Onochie wanda ta na cikin masu ba Shugaban kasa Buhari shawara tace irin su Diezani sun sace kudin kasa su na kuma kokarin dawowa domin gujewa shari'a a Najeriya. Onochie yace kasar Amurka da sauran kasashen Turai na neman ta don haka zai yi wahala ta sha a hannun shari'a.

Kwanaki ta caccaki Uwargidan Najeriya Patience Jonathan bayan da tace Hukumar EFCC ta shafa mata lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel