Wani na kusa da Shugaban Kasa yayi korafi game da Gwamnatin Buhari

Wani na kusa da Shugaban Kasa yayi korafi game da Gwamnatin Buhari

- Wani yayi korafin cewa Shugaba Buhari ya rabu da mutanen Kano

- A cewar sa duk irin kokarin da Yankin yayi an manta da su yanzu

- A lokacin zabe dai Jihar Kano ta fi ko ina ba APC kuri'a a Kasar

Daya daga cikin wadanda su ka taya Shugaban kasa Buhari lashe zabe ya koka game da Gwamnatin na Buhari.

Wani na kusa da Shugaban Kasa yayi korafi game da Gwamnatin Buhari

Dandazon siyasa wajen taron Buhari

A cewar Abdurrasheed Ahmad Liman duk da irin kokarin da mutanen Kano su kayi wa Jam'iyyar APC an ware su a wannan Gwamnatin. Ahmad Liman yace irin su Legas su na cabawa yayin da babu wani aikin kirki da Gwamnatin Buhari ta shiryawa Jihar Kano.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta saba alkawarin ta Inji Matasan Arewa

Ahmad Liman yace Legas ta samu fiye da kowa a tafiyar daga cikin kasafin kudi zuwa yarjejeniyar da Shugaban kasa Buhari ya sa hannu da Kasar China. Yace tun bayan da aka yi zabe Gwamnatin Shugaban kasar ta rabu da su.

Haka nan kuma ya koka da cewa Shugaba Buhari bai taba taka kafa a Jihar Kano ba bayan yayi watsi da Jihohin da su kayi masa kokari irin su Jigawa, Katsina da sauran su. Liman yana cikin kwamitin APC da su ka taya Buhari cin zabe a 2015.

Liman ya kara bayyana cewa kaf Arewacin kasar abin da su ka samu daga a kasafin kudin kasar bai kama hanyar abin da Yankin kudu su ma samu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel