Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

Shugaban hukumar tace albarkatun man fetur ta kasa, Maikanti Baru ya mayar da martani ga zarge zargen da karamin ministan mai, Ibe Kachikwu yayi masa, cikin wata wasika daya aika ma shugaban kasa.

Maikanti ya bayyana cewa ya ga dacewar mayar da martanin ne bayan umarni daya samu daga fadar shugaban kasa na yin hakan, inda yace zargin da ministan ke yi masa basu da kai ko gindi.

Baru yayi wannan martani ne cikin wata sanarwa da hukumar NNPC ta fitar a ranar Litinin 9 ga watan Oktoba a ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

KU KARANTA: Rayuwar Mata a yankin Arewa na cike da ƙalubale masu tarin yawa – Inji Rahama Sadau

Dangane da zargin rashin mika wasu kwangiloli da Baru yayi ga kwamitin gudanarwar NNPC don su tattauna yiwuwar kwangilar ko akasin haka, Baru yace dokokin NNPC basu bukaci shugaban NNPC ya aika da kwangiloli ga karamin minista ko kwamitin gudanarwar NNPC ba.

Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

Maikanti Baru

“Abinda doka ta tanadar shine a mika takardun bada kwnagilar ga kwamitin duba kwangiloli na NNPC, ko shugaban kasa ko kuma babban minista, ko kuma majalisar zartarwa domin su tantance tad a kuma bada izini.” Inji Baru.

Baru bai tsaya nan ba sai daya ce “Akwai wasu lokutta ma wanda izinin kwamitin duba kwangila an NNPC kadai ake bukuta wajen bada kwangila, a wasu lokuta kuma akai ma shugaban kasa ko kuma majalisar zartarwa don samun izini.

“Ko a maganan yarjejeniyar hakar mai da kuma na siya da siyar da mai da muka shiga don bada kwangilar ayyukan, bamu sanya wani farashi ba, ba kamar yadda karamin minista Kachikwu yayi zargin wai mun bada kwangilolin akan kudi dala biliyan 10, da biliyan 15 ba, balle kuma har a ce wai mun wuce gona da iri.”

Daga karshe Baru ya musanta zargin rashin da’a da kuma neman jin ta bakin ministan kafi ya gudanar da ayyuka kamar su bada kwangila, inda yace a duk lokacin da NNPC zata bada kwangila, sai ya tuntubi ministan, inji majiyar NAIJ.com.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel