Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa laifin sayar da jariri kan naira N605,000

Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa laifin sayar da jariri kan naira N605,000

- Kotu ta ba da belin wata matar da ta sayar da jaririn ta kan kudi naira N605,000

- An zargi matar da laifin hada kai da wasu mutane wajen sayar da jariri mai tsawon watanni 4 da haihuwa

- An sayar da jaririn ne a jihar Enugu

Wata kotun Majistare dake Minna ta ba da belin wata matar aure, mai suna Eucharia Mba, da aka kama kwanakin baya bisa zargin sayar da jaririnta wanda ya kai watanni 4 da haihuwa a farashin naira N605,000.

An kama Mba tare da wani Bright dake unguwar Chanchanga a Minna da wani Peter Ani.

Wadanda su ke fuskantar laifin yaudara, siya da sayar da jariri.

Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa laifin sayar da jariri naira N605,000

Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa laifin sayar da jariri naira N605,000

Wannan laifi ya saba wa sashe na 79 da 278 na dokar kasa.

KU KARANTA : Babu tsoron Allah a gina cocina a ko ina – Kadinal Okogie

A jawabin da aka samu daga rahoton yansanda, wani mista John dake zama a unguwar Mechanic Junction Chanchanga, ya kawo ma hukumar yansada kara a watan Satumba 2017 da ce wa wata Amaka Bright dake zama a unguwar da Brihgt Ahuruezeanya sun hada kai da matar sa sun sayar da jaririn su wanda ya kai watanni 4 da haihuwa.

An zargi Eucharia da sauran mutane 2 da sayar da jariri a jihar Enugu ma wani Mista Ani akan farashin naira N605,000.

Masu laifin sun karayata zargin da aka mu su a kotu.

Alkalin kotun majistare, Hassan Mohammed ya ba da belin matan 2 saboda rashin lafiya. Daya ta na da juna biyu na tsawon watanni 8, daya kuma ta na shayar da jariri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel