Jam’iyyar APC ta caccaki Galadima bisa kira da yayi akan ta

Jam’iyyar APC ta caccaki Galadima bisa kira da yayi akan ta

- Jam'iyyar APC ta caccaki wani jigonta Buba Galadima

- Hakan ya biyo bayan furuci da yayi na cewa bata cancanci zama jam'iyya ba

- Jam'iyyar ta jadadda cewa tayi wannan zama da Galadima ke nufi a shekarar 2014

Jam’iyyar APC ta caccaki jigon ta, Alhaji Buba Galadima bisa ikirarin da yayi kwanan nan na cewa ya kamata a karda ayi ma jam’iyyar rijista saboda kasa yin taron kungiyar amintattu ko sau guda.

A makon da ya gabata Galadima ya bayyana cewa abun kunya ne ace jam’iyya mai ci ta kasa gudanar da taron kwamitin amintattu na jam’iyyar ko sau guda.

Da suke maida martani, wani mamba na kungiyar Amintattu na jam’iyyar, Cif Sam Nkire, a wata sanarwa da yayi a Abuja, a jiya, yace kungiyar amintattu na jam’iyyar APC ta fara gudanar da zamanta na farko a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta 2014, a masaukin sabon gwamnan jihar Rivers, Adokoro-Abuja, wanda shi kansa yana daga cikin wadanda suka halarta.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babu abin da zai hana mu cin zabe Inji Osinbajo

A cewar jigon na APC, sauran wadanda suka halarci zaman a wannan rana sun hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Atiku Abubakar, Cif John Odigie-Oyegun, Asiwaju Bola Tinubu, Cif Bisi Akande, Dr. Ogbonnaya Onu, Dr. Musa Rabiu Kwankwaso, Dr. Chris Ngige, Owelle Rochas Okorocha da kuma Cif Tony Momoh, harda kuma gwamnoni masu ci da tsofaffin gwamnoni na mulkin soja da farar hula.

Sanarwan ta kuma nuna cewa jam’iyyar na kokarin sake sunan kungiyar ta na amintattu zuwa kungiyar dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel