Fasto ya kashe daliban koyan aikin Nas da wuka

Fasto ya kashe daliban koyan aikin Nas da wuka

- Zargin sata ya sa wani fasto ya kashe wata yarinyar

- Callista da zargi diyar fasto Jehova da sace butur da cajar waya

- Jami'an yansanda a jihar Imo sun kama faston Esom Jehova da laifin kisan kai

Rundunar yan sadan jihar Imo, sun kama wani fasto na cocin Assemblies of God mai suna Esom Jehovah, bisa zargin kashe wata daliban koyon aikin Nas da wuka.

Marigayiyar mai suna Callista, ta tunkari Faston ne akan neman batur da cajar wayar da aka bata ta yi caji.

Fasto ya kashe daliban koyan aikin Nas da wuka

Fasto ya kashe daliban koyan aikin Nas da wuka

Wani shaida mai tushe ya fada ma yan jaridar Sun cewa, wani yaro dake gidan da Callista ta ke zama ya bata batur da cajar wayar sa ta taya caji, sai babbar diyar Fasto Esom Jehovah ta sace abubwan, wanda aka gani kwana biyar bayan aukuwan wannan mumunar lamari.

KU KARANTA : Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

“Fushin zargin sata da Callista ta yi wa diyar sa, ya sa faston ya kama ta da duka, ana cikin haka, diyar ta dauka wuka ta caka wa Callista a baya, a lokacin da mahaifin ya kwantar da ita yana duka.”

NAIJ.com ta samu rahoton cewa yarinyar faston mai shekaru 21 ta gudu, shi kuma mahaifinta Fasto Jehovah ya shiga hanun yansanda a lokacin da shima yake kokarin tserewa.

Yansada sun garzaya da gawar Callista dakin ajiye gawa dake asibitn Holy Rosmary a jihar Imo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel