Kalli yadda Sanatan Najeriya yake facaka da kuɗi wajen siyan motoci18 na alfarma (Hotuna)

Kalli yadda Sanatan Najeriya yake facaka da kuɗi wajen siyan motoci18 na alfarma (Hotuna)

- Sanatoci na cigaba da nuna ma yan Najeriya tarin arzikin da ake samu a majalisar dattawa

- Sanata Dino Melaye yayi bajakolin motocinsa na alfarma

Sanata Dino Melaye dake wakiltar al’ummar Kogi ta yamma yayi bajakolin motocinsa na alfarma guda dai dai har goma sha takwas a shafins na Instagram.

NAIJ.com ta ruwaito Sanatan da baya rabuwa da shiga bakin jama’a yayi ma hotunan motocin taken ‘Kayan wasa na, abin so na, duk zaku fada, ku fada.’

KU KARANTA: Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani

Kalli yadda Sanatan Najeriya yake facaka da kuɗi wajen siyan motoci18 na alfarma (Hotuna)

Dino Melaye

Wasu daga cikin motocin da Dino Melaye ya daura hotunansu sun hada da G-Wagon, Rolls Royce, Bentley, Ferrari da sauran manyan motocin alfarma da kudadensu sai dai dinga lissafin daruruwan miliyoyi.

Motocin

Kalli yadda Sanatan Najeriya yake facaka da kuɗi wajen siyan motoci18 na alfarma (Hotuna)

Sai dai hakan ya takulo ra’ayoyi daban daban daga yan Najeriya, inda wasu suka tofa albarkacin bakinsu kamar haka; wani cewa yayi, "kana siyan abinda baka da bukatarsu, amma ka sani alfahari ba burgewa bane."

Kalli yadda Sanatan Najeriya yake facaka da kuɗi wajen siyan motoci18 na alfarma (Hotuna)

Motocin

Wani ma’abocin Instagram mai suna Benjisazi cewa yayi “Ba zan taba kiranka barawo ba, don kuwa nima so nake nayi kudi kamar ka, kuma ina so in yi suna a siyasan Najeriya, don haka a cigaba da gashi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yunkurin yi ma sanata Dino Melaye kiranye, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel