Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

- Rundunar yansadar Kaduna sun fito zanga-zagna akan rashin biyan su albashi

- Hukumomin yansanda na jihohi 8 suna bin jami'an yansanda albashin watanni 2

-Jam'ian yansada sun zargi Kemi Adeosun da rashin fada wa shuagabn kasa gaskiyan al'amarin alabshin yansada a Najeriya

Jami’an yansadar a jihar Kaduna suna kan yin zanga zangar lumana saboda rashin biyan albashin su na watan Agusta da na Satumba.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa hukumomin yansanda na jihohi 8 wanda ya kunshi Kaduna, Kebbi Gombe, Nasarawa, Ekiti ,Bayelsa, Imo da Ogun suna bin jami’o’in su alabshin watan Agusta da Satumba.

Zanga-zangar wanda ya kunshi manyan ofisoshin yansada da kananan, ya samu halarta sama da yansada 2000 wanda suka yi dandazo a gaban ofishin biyar albashi da ke shelkwatar hukumar yansadar na jihar.

Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

Jami'an yansandar Najeriya sun shiga zanga-zanga akan rashin biyan su albashi

Kwamishinan yansadar Jihar, Cyril Abeh, ya ce matsalar rashin biya albashi daga mai’akatar kudi ne ba daga hukumar yansada ban, kuma yayi kira da ofisoshin yansadar jihar da su dakatar da zanga- zangar.

KU KARANTA : Senatocin Najeriya sun fi Trump, da firayam Ministar UK yawan albashi – Oyebola

“Aikin dan sanda ya kushi bin doka da oda, duk dansandar da ya karya doka zai fuskanci horo. Yanzu haka na halarci wata taron ne, amma ina kan hanyar komawa shelkwata dan shawo kan matsalar,” inji shi.

Wasu jami’an yansanda sun zargi ministar harkan kudi Kemi Adeosun akan boye wa shugaban kasa Muhammadu Buhari asalin abun da ke faruwa da albashin yansada a kasar.

“Ta yi wa shugaban kasa karya cewa abubuwa suna kyau. Ta yaya zaka yaki cin hanci da rashwa idan baka biya dansanda albashin sa na wata biyu ba, " inji wani dansanda da yan jarida suka zanta dashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel