Sojoji sun hallaka yan Boko Haram guda 2, sun ƙwato buhun masara guda 2

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram guda 2, sun ƙwato buhun masara guda 2

- Sojojin Najeriya sun yi karanbatta da yan ta'addan Boko Haram

- An kashe yan ta'adda 2, sauran sun ruga da raunuka a jikinsu

Rundunar Sojojin Najeriya dake yawo ka babur ta samu nasara akan mayakan Boko Haram yayin gudanar da aikin da take yin a musamman da nufin kakkave ragowarsu daga yankin Arewa maso gabas da kuma kasa baki daya.

Mataimakin Kaakakin rundunar, Laftanar Kingsley Samuel ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar, a daren Lahadi 8 ga watan Oktoba, inda yace da misalin karfe 10 na daren Juma’a 6 ga watan Oktoba ne Sojojin suka shirya kwantan bauna kan mayakan.

KU KARANTA: Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani

Sojojin sun ci tarar yan Boko Haram dinne yayin da suke kokarin tsallakewa zuwa Dajin Sambisa daga kauyen Mayanti, cikin karamar hukumar Bama, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram guda 2, sun ƙwato buhun masara guda 2

Buhun masara guda 2

Yayain arangamar, Sojojin sun kashe yan Boko Haram guda 2, tare da jikkatan sauran da suka ranta ana kare bayan sun zubar da makamansu. Haka zalika Sojojin sun kwato buhhunan masara guda 2.

Ita dai wannan runduna ta musamman mai amfani da babur ta samu sa albarkan babban hafsan Sojin kasa, laftanar kanar Tukur Yusuf Buratai ne, wanda ya kaddamar da ita da nufin karfafa yaki da ta’addanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel