IPOB : An nemi kotu ta ba da umarnin kama Nnamdi Kanu

IPOB : An nemi kotu ta ba da umarnin kama Nnamdi Kanu

- Kenneth Ogochukwu ya shigar da karar shugaban IPOB Nnamdi Kanu a kotu

- Oguchukwu ya ce guduwar Nnamdi Kanu zuwa kasar Britaniya ya saka senata Eyinaya Abaribe ciki tsaka mai wuya

- Shugaban hukumar shiga da fice na Najeriya da kwamshinan ofishin jakadar kasar Britaniya za su gurafana a gaban kotu

An bukaci wata babban kotu tarayya dake Abuja da ta ba offishin jakadancin Britaniya da hukumar shige da fice a Najeriya umarnin kama shugaban kungiyar yan asalin Biyafara Nnamdi Kanu, da dawo da shi kasar Najeriya daga kasar Britiniya dan gurfanar da shi a gaban hukuma.

Wani Ugochukwu Kenneth ya shigar da karar sa a kotu ta lauyoyin sa, Barrista Obor John da Tersagh Unande akan neman Ministar sharia Abubakar Malami ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da yasa Ofishin jakadancin kasar Britaniya ta dawo da Nnamdi Kanu Najeriya.

Kwamishinan ofishin jakadancin Britaniya, da shugaban hukumar shiga da fice na Najeriya za su gurfana a gaban Jastis John tsoho a safiyar gobe dan kare kan su.

IPOB : An nemi kotu ta ba da umarnin kama Nnamdi Kanu

IPOB : An nemi kotu ta ba da umarnin kama Nnamdi Kanu

Mai daukaka kara Kenneth Ugochukwu, ya ce guduwar Nnamdi Kanu zuwa kasar Britaniya ya saka senata mai wakiltar kudancin Abia Eyinaya Abaribe cikin tsaka mai wuya, saboda shi ya tsaya ma sa lokacin da aka ba shi beli.

KU KARANTA : Biyafara : Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana IPOB a matsayin yan ta’ada

Ya ce “babu yadda za ayi Nnamdi Kanu ya tsere daga Najeriya zuwa kasar Britaniya ba tare da sanin hukumar shiga da fice na Najeriya ba da kuma ofishin jakadancin kasar Britaniya da ake zargin su da taimaka ma masa wajen gudu wa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel