Mai kan uwa da wabai: Ýan bindiga sun bindige mutane 10 a jihar Ribas

Mai kan uwa da wabai: Ýan bindiga sun bindige mutane 10 a jihar Ribas

Wasu gungun yan bindiga sun afka babban birnin jihar Ribas, Fatakwal a daren Litinin 9 ga watan Oktoba, inda suka bude kan jama’a tare da kashe mutane 10.

Rahotanni sun bayyana cewar yan bindiga sun isa unguwar Mgbosimiri ne da misalin karfe 4 na dare, inda suka bude wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar shiga halin firgici da jama’an unguwar suka yi.

KU KARANTA: Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani

Jaridar Punch ta ruwaito har yanzu ba’a tabbatar da musabbabin kai hare haren ba, inda wasu ma’aurata, sababbin aure suma suka rasa rayukansu.

Mai kan uwa da wabai: Ýan bindiga sun bindige mutane 10 a jihar Ribas

Ýan bindiga

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar harin, amma yace babu wasu tantattun bayanai game da hari zuwa yanzu.

Amma KaakaKin ya bada tabbacin kokarin da rundunar Yansandan jihar keyi na ganin ta kamo wadanda suka kai harin, da duk wasu dake da hannu cikin kai harin, kuma zata tabbatar an yi musu hukunci daya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yadda tsageru ke kai ma jama'a hari, kalli NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel