Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani

Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani

Wani bahillace makiyayi, Auwalu Idi ya fuskanci hukuncin zaman gidan kaso bayan da aka kama shi da shanu guda 22 wanda ake zargin ya sace su ne, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an saci dabbobin ne yayin da wasu yan fashi da makami suka diran ma wani dajin da ake kiwon dabbobin a jihar Zamfara, kamar yadda Yansanda suka bayyana ma kotu.

KU KARANTA: Rikicin Biyafara: Attahiru Bafarawa ya gargaɗi shugaban Buhari, ‘ Ba kan ka farau ba’

Dansanda mai kara ya shaida ma wata Kotu a jihar Katsina, dake karkashin Alkali Abdulkareem Umar cewa a lokacin da aka yi satar, Auwalu Idi baya nan, haka ta sa ake zarginsa da hannu cikin fashin da aka yi.

Wani Bafulatani da yayi zari, ya saci shanu 22 ya fuskanci hukunci mai tsanani
Shanu

Ana tuhumar Idi da laifin hadin baki don aikata mummunan laifi, cin amana da kuma fashi da makami kamar yadda Dansanda mai kara ya shaida ma alkalin Kotun, amma shi wanda ake zargi ya shaida ma Kotu cewa an kama shi ne yayin dayake cikin neman wata dabbarsa a cikin Daji a daidai lokacin da aka sace shanu 22.

Sai dai Yansanda kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa Idi ya siyar da dabbobin ne a kasuwar Danmusa a kan N133,000, kuma tuni har ya mika ma mai dabbobin kudaden bayan ya sha tambaya a hannun Yansanda.

Rahoton Yansanda ya nuna cewa a ranar 17 ga watan Satumba da misalin karfe 1:30 na dare ne Yan fashi suka dira garken shanun, inda suka tarar da yaron mai shanun, Lawal Sani mai shekaru 20, kuma suka ji masa rauni, sa’annan suka kada dabbobin.

Daga karshe, Alkali Umar ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Rikicin jam'iyyar PDP ya ta'azzara, kalla a Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel