Hukumar ‘yan sanda ta cafke wasu malaman addinni 3 da sassan jikin mutum

Hukumar ‘yan sanda ta cafke wasu malaman addinni 3 da sassan jikin mutum

- Hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wasu mutane 3 da sassan jikin mutum

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce an kama mutanen a ranar 5 ga watan Oktoba

- Kwamishinan ya ce a kan tambayoyi mutanen sun bayyana kansu a matsayin masu kisan gilla

Hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wasu mutane 3 wadanda suka yi ikirarin cewa su malaman Islama ne akan zargin kisan kai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Ilyasu, wanda ya bayyana wadanda ake zargin a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba a hedkwara hukumar a Abeokuta babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce an kama su ne a ranar 5 ga Oktoba da sassan jikin mutum.

Hukumar ‘yan sanda ta cafke wasu malaman addini 3 da sassan jikin mutum

Mutane 3 da aka kama da sassan jikin mutum

Ilyasu ya ba da sunan mutanen a matsayin Adebayo Mudashiru mai shekaru 36 da haihuwa da Raheed Abass, 33 da kuma Rasaq Adenekan, 42, inda suka kama su da sassa daban-daban na jikin mutum da dabbobi masu rarrafe da kuma laloyi.

KU KARANTA: Rundunar Sojin Kasa ta sanar da ranar kammala Rawar Mesa II

Mista Ilyasu ya bayyana cewa a kan tambayoyin da aka yiwa wadanda ake tuhuma sun kasance masu kisan gilla, tare da ofishin su a No. 6 Baase Compound wanda ke Totoro a Abeokuta.

Yayin da wadannan mutane 3 da ake zargi suke magana da jaridar PREMIUM TIMES sun yi ikirarin cewa su "alfa" ne wato malaman addinin Islama. Sun bayyana cewa sun shiga cikin al'amuran don magance matsalolin abokan ciniki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel