Rikicin Biyafara: Attahiru Bafarawa ya gargaɗi shugaban Buhari, ‘ Ba kan ka farau ba’

Rikicin Biyafara: Attahiru Bafarawa ya gargaɗi shugaban Buhari, ‘ Ba kan ka farau ba’

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa yayi tsokaci game da rikicin kungiyar a ware donkafa kasar Biyafara, mai suna IPOB, inji jaridar Daily Post.

Bafarawa ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buharia a kan amfani da karfin Soja wajen murkushe masu fafutukar kafa kasar ta Biyafara, inda yace ai ba a kansa aka fara samun haka ba.

KU KARANTA: Allah ya yiwa mataimakin shugaban APC a Zamfara rasuwa

“Lokacin da Obasanjo ke shugaban kasa, an samu rikicin Shari’a, kum da aka gano tsohon gwamna Yarima Bakura ne uban tafiyar, sai aka baiwa Obasanjo shawarar ya murkushe shi, amma Obasanjo ya ki, ya kira shi aka sasanta.

Rikicin Biyafara: Attahiru Bafarawa ya gargaɗi shugaban Buhari, ‘ Ba kan ka farau ba’

Attahiru Bafarawa

“Haka shima Yar’adua a zamaninsa, ya tarar da matsalar yan Neja Delta, shima haka ya gayyaci shuwagabanninsu, aka tattauna aka gano bakin zaren, amma yanzu sai ga Buhari yazo ya fara diran ma yan IPOB, bayan kamata yayi a sulhu a irin tsarin dimukradiyya.”

Attahiru Bafarawa ya bada tabbacin jam’iyyar PDP zata kayar da APC a zabukan 2019, matukar an yi shi cikin gaskiya ba tare da rinto ba, ya kara da cewa daga kasafin kudin badi, Buhari ba zai sake shirya wani ba, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito

“Dama na san babu wani abin alheri da gwamnatin nan zata tabuka, don haka bani mamakin yadda gwamnatin ke tafiyar hawainiya. Na san babu wani banbanci tsakanin APC da PDP, saboda duk tsofaffin yayan PDP ne suka kafa APC.”

“Wannan kasafin kudin badi da ake shiryawa, shine zai zama kasafin kudi na karshe da gwamnatin Buhari zata yi, ko a kasafin kudin bana ma, bamu ga komai ba. Duk wata gwamnati mai hankali ya kamata ace tun a shekarun 2 na mulkinta an gani a kasa.” Inji Bafarawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Farashin man fetur ya karye, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel