Senatocin Najeriya sun fi Trump, da firayam Ministar UK yawan albashi – Oyebola

Senatocin Najeriya sun fi Trump, da firayam Ministar UK yawan albashi – Oyebola

- Oyebola ya soki yan majalissun Najeriya akan yawan albashi da suke ansa

- Cif Areoye ya ce yan majalissun Najeriya ba su iya aiki ba duk da yawan albashin su

- Abun takaici ne a ce duk da tsanani talauacin da yan Najeriya suke ciki senata daya yana ansa albashin dala milyan $1.7m ko wani shekara inji Oyebola

Shugaban kungiyar gyara da kawo cigaba a Najeriya, Cif Areoye Ayebola, ya caccaki yan majallisar Najeriya akan yin kunnen uwar shegu game da kiran da yan Najeriya suke mu su na rage albashin su.

Oyebola ya ce tona asarin yan majalissu da shugaban kwamitin ba wa fadar shugaban kasa shawara akan cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay (SAN) yayi akan albashin su, ya kara janyo hankalin mutane akan kiraye kirayen da aka mu su a shekaru baya game da rage albashin su.

“Abin takaici ne da kuma rashin tausayi a ce, duk da tsanin talauci da yan Najeriya ake fuskanta a Najeriya, senata daya yana ansa albashin dala miliyan $1.7m, wanda yafi albashin shugaban kasar Amurka a shekara da dala $400,000. Wanda kasar Amurka ta fi Najeriya a arziki a kusan kowani fanni. Mamba daya na majalissar dodoki Najeriya ya fi shugaban kasar Amurka yawan albashi.

Senatocin Najeriya sun fi Trump, da firayam Ministar UK yawan albashi – Oyebola

Senatocin Najeriya sun fi Trump, da firayam Ministar UK yawan albashi – Oyebola

“Kuma duka yan majalissar dokoki sun fi Firayam ministar kasar Britaniya yawan albashi, bayan dan majalissa a kasar Ghana yana ansa kasa da haka.

KU KARANTA : Fani Kayode ya zargi sojoji da kwashe kaya gidan Nnamdi Kanu

Wasu tsirarun yan majalissar dokoki a Najeriya suna ansan sama da naira miliyan N10m a kowani wata.

“Miliyoyin kudaden da senatoci da yan majalissar dokoki suka ansa da sunan albashi abun takaici ne da rashin tausayi,” inji shi.

Oyebola yace "duk da albashin da ake biyan yan majalissun kasar Ghana wanda bai kai yawan albashin yan majalissar Najeriya ba, sun fi yan Najeriya iya aiki da kawo ma kasar su cigaba, kuma ba sa fashin zuwa aiki, “ sun zama abun koyo ga kasashe dayawa a Afrika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel