Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari, laifin sa ne - Dakta Aminu Gamawa

Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari, laifin sa ne - Dakta Aminu Gamawa

Wani babban lauya a Arewacin Najeriya mai suna Dakta Aminu Gamawa ya soki Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kaikaice inda yake nuna duk matsalar da ake samu a halin yanzu laifin shugaba Buhari ne ba wai na mukarraban sa bane kamar yadda wasu ke gani.

Babban Lauyan yayi wannan ikirari ne a shafin sa na Tuwita lokacin da yake yin tsokaci game da yadda shugaban ke ta nada kwamitoci barkatai duk kuwa da cewa baya anfani da rahoton da suka gabatar masa.

Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari, laifin sa ne - Dakta Aminu Gamawa

Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari, laifin sa ne - Dakta Aminu Gamawa

KU KARANTA: Sojoji sun sanar da ranar fara wani muhimmin shirin samar da zaman lafiya

NAIJ.com dai ta samu cewa Dakta Gamawa ya fada cewa: "Meye anfanin kafa kwamitoci barkatai idan har an san ba zai anfani da rahoton su ba?"

Haka zalika ya kara da cewa: "Kamata yayi kawai idan ana zargin wani jami'in Gwamnati da laifi to a mika shi ga hukumomin tsaro ba wai ayi ta yamadidi da maganar ba ta hanyar kafa kwamitin bincike."

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya shugaba Buhari ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin sa Farfesa Osinbajo na nufin bincikar sakataren Gwamnatin sa da ake zargi da wata babbar badakala amma har yanzu shuru ba wani matakin da aka dauka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel