Shugaban yan Sandan Najeriya ya fi karfin mu - Hukumar gudanarwa

Shugaban yan Sandan Najeriya ya fi karfin mu - Hukumar gudanarwa

Hukumar gudanarwa ta yan sandan Najeriya watau Police Service Commission (PSC) a turance tace kundin tsarin mulki bai ba ta damar da zata iya ladabtar da shugaban hukumar rundunar yan sanda ba.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a da kuma yada labarai na hukumar Mista Ikechukwu ya fitar inda yace hukumar gudanarwar ba zata fita daga cikin hurumin ta ba da kundin tsarin mulkin kasar ya gindaya mata ba.

Shugaban yan Sandan Najeriya ya fi karfin mu - Hukumar gudanarwa

Shugaban yan Sandan Najeriya ya fi karfin mu - Hukumar gudanarwa

KU KARANTA: Gwamna Elrufa'i ya bayyana wanda zai marawa baya a 2019

NAIJ.com ta samu dai cewa a cikin sanarwar, Mista Ikechukwu ya bayyana ce: "Duk da cewa dai hurumin mu na aiki sun hada da nadawa, habbakawa da kuma ladabtarwa ga rundunar yan sandan kasar, amma hakan bai sa hadda shugaban rundunar ba."

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Sanata Misau mai wakiltar mazabar jihar Bauchi ta tsakiya a satin da ya gabata ya yi zargin cewa shugaban yan sandan Najeriya IGP Ibrahim Idris ya karya dokar yan sandan kasar yayin da ya yi wa wasu jami'an hukumar ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel