Rikita-Rikita: Majalisar dokokin jihar Jigawa na shirin tsige Gwamna Badaru

Rikita-Rikita: Majalisar dokokin jihar Jigawa na shirin tsige Gwamna Badaru

A halin yanzu dai tuni hankula suka gama tashi bisa wata makarkashiyar da mambobin majalisar jihar Jigawa ta Arewa maso yamma take shiryawa Gwamnan jihar da nufin tsige shi daga mukamin sa.

Majiyar mu da ta tattaro mana cewa yan majalisar sun fara shire-shiren tsige Gwamnan ne a bisa wani zargi da suke yi masa na sayar da wata babbar kadarar jihar dake a jihar Legas ba bisa ka'ida ba.

Rikita-Rikita: Majalisar dokokin jihar Jigawa na shirin tsige Gwamna Badaru

Rikita-Rikita: Majalisar dokokin jihar Jigawa na shirin tsige Gwamna Badaru

KU KARANTA: Sojoji sunyiwa gidan Nnamdi Kanu kar kaf

NAIJ.com ta samu cewa a satin da ya kamata ne ma dai majalisar dokokin ta jihar ta kafa wani kwamitin bincike na ta da ta dorawa alhakin yayi kwakkwaran bincike a bisa abun da suka kira aikata ba dai-dai ba da Gwamnan yayi wajen ba kananan hukumomin jihar damar siyen kujerun zama.

Da yake karin haske game da lamarin, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dutse a Musa Sule da kuma yake zaman shugaban kwamitin binciken ya bayyana Gwamnan a matsayin wanda ya karya doka idan dai har aka same shi da laifin yin hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel