Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin zama a gida domin kauracewa zaben gwamna a jihar Anambra ranar 18 ga watan Nuwamba

Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin zama a gida domin kauracewa zaben gwamna a jihar Anambra ranar 18 ga watan Nuwamba

- Za a yi zaben gwamna a jihar Anambra ranar 18 ga watan Nuwamba mai kamawa

- Kungiyar IPOB ta bukaci duk 'yan kabilar Igbo su zauna a gida domin kauracewa zaben

- Sunyi zargin cewar gwamnati ta kama tare hallaka shugaban su Nnamdi Kanu

Haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta IPOB ta yi inkarin cewar zaben gwamna a jihar Anambra da za ai 18 ga wata ba zai yiwu ba, sannan ta umarci 'ya'yanta da ragowar masu yakin neman 'yanci da su zauna a gida domin kauracewa zaben.

Sakataren yada labarai na kungiyar ta IPOB, Emma Powerful, ya bayyana cewar zaben gwamnan mai zuwa tamkar jarrabawa ce ga fafutikar da kungiyar ke yi. Kungiyar ta ce dole su nunawa 'yan siyasar yankin cewar kudi ba zai saye su ba.

Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin zama a gida domin kauracewa zaben gwamna a jihar Anambra ranar 18 ga watan Nuwamba

Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin zama a gida domin kauracewa zaben gwamna a jihar Anambra ranar 18 ga watan Nuwamba

"Duk wani mai kishin BIYAFRA dake neman 'yanci daga hannun musulmi Hausa Fulani da suka kankanen mulkin Najeriya ba zai fito domin kada kuri'a ranar zaben ba, hakazalika ba zai bari na kusa da shi ma su fita domin kada kuri'a ba. Ranar 18 GA watan Nuwamba zata kasance rana mai matukar tarihi". A cewar jawabin.

Jawabin ya kara da cewa "Kauracewa zaben zai tabbatarwa duniya cewar da gaske muke a kan yunkurin mu na kafa kasar Biyafra, sannan zai zama sako ga gwamnati cewar babu abinda zai dakatar da kafa kasar Biyafra. Idan mukayi nasarar yin haka a jihar Anambra sai kuma mu saka rana a shekara mai zuwa ta ballewa daga Najeriya ko da kuwa gwamnatin tarayya bata amince ba. Abinda ya faru da Kataloniya a kasar Sifen da kuma Kurdawa a kasar Iraqi ya ishemu darasi cewar zamu iya yagewa daga Najeriya ba tare da yardar gwamnati ba".

Kungiyar ta bayyana cewar a yayin da duniya ke kallon abinda yake faruwa a Najeriya, basu da wata hanya da zasu tabbatarwa da duniyar cewar da gaske suke a kan kudirin su, da ya wuce su kauracewa zaben.

DUBA WANNAN: Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

Kungiyar ta IPOB ta ce kauracewa zaben zai zama wata hanya ta nuna fushin su da kuma nuna kishin su ga shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu, da ragowar 'yan kabilar Igbo da suka ce sojoji sun hallaka, sannan kuma su kunyata Shugabannin yankin dake nuna goyon bayan su ga gwamnati wadan da suka ce sun fifita abin duniya a kan 'yan uwan su.

Kungiyar ta ce duk da amfani da kudi da kafafen yada labarai da gwamnati ke amfani da su wajen bata masu suna ba zasu saurara wajen aikewa da sako ga gwamnati da kuma duniya baki daya ba cewar fafutikar Biyafra halastacciya ce kuma ba zata taba gushewa ba

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel