Fani Kayode ya zargi sojoji da kwashe kaya gidan Nnamdi Kanu

Fani Kayode ya zargi sojoji da kwashe kaya gidan Nnamdi Kanu

- Fani Kayode ya zargi sojoji da kwashe kayan gidan su Nnamdi Kanu

- Tsohon ministar ya ce har da kayan sawan shuagaban IPOB sojoji suka kwashe

- Har yanzu babu wanda ya san inda shugaban IPOB yake bayan harin da sojoji suka kai gidan sa

Tsohon ministar sufurin jirgin sama, Femi Fani Kayode, yace a yanzu haka sojoji suna kan kwashe kayan gidan shugaban kungiyan yan asalin Biyafara IPOB Nnamdi Kanu.

Fani-Kayode ya zargi sojojin da kwashe kayan gidan shugaban IPOB wanda ya kunshi kujeru, kayan lanatarki, da kayan sawan sa.

Sojoji suna kan kwashe kayan gidan Nnamdi Kanu – Fani Kayode

Sojoji suna kan kwashe kayan gidan Nnamdi Kanu – Fani Kayode

Tsohon ministar yayi wannan zargin ne a shafin sa na sa da zumunta na tuwita.

KU KARANTA : An kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu saboda bashin Naira N7,500

Ya rubuta kamar haka “Sojoji suna kan kwashe kayan gidan Nnamdi Kanu wanda ya kunshi kujeru talabajin, kayan sawan sa da sauran su. Mai yasa haka?,” inji shi.

Har yanzu babu wanda ya san inda shugaban IPOB yake tun lokacin da sojoji su ka kai hari gidan su a ranar 14 ga watan Satumaba 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel