Buhari zaiyi sulhu tsakanin Baru da Kachikwu, Inji shugaban VON

Buhari zaiyi sulhu tsakanin Baru da Kachikwu, Inji shugaban VON

- Mista Osita Okechukwu ya yabbawa salon mulkin shugaba Buhari

- Babban direktan na muryar Najeriya yayi imani cewa Shugaba Buhari zai sulhunta Karamin ministan man fetur da shugaban hukumar NNPC

- Daga karshe Okechukwu yace shugaba Buhari mutum ne da ke mutunci a idon duniya kuma bazai yarda wani ya zubar masa da mutuncin ba

Babban Direktan muryar Najeriya (VON), Mista Osita Okechkwu ya tabbabatar wa 'yan Najeriya cewa Shugaba Buhari zaiyi sulhu tsakanin karamin Ministan man fetur, Ibe Kachikwu da Shugaban hukumar NNPC Dr. Baru Maikanti.

Okechukwu ya fadi wannan maganar ne lokacin da yake magana da manema labarai a garin Enugu bayan da farko bai so yin tsokaci kan maganar ba tunda ba shine mai magana da yawun shugaban kasan, yace shugaban Buharin zaiyi duk mai yiwuwa domin kare mutunci da kimar da yake dashi a idon al'ummar Najeriya da ma duniya baki daya.

Ya kara da cewa zaman tattaunawa da shugaba Buhari yayi tare da Kachikwu ya nuna cewa wasikar Kachikwu ta isa wurin shugaba Buhari.

Buhari zaiyi sulhu tsakanin Baru da Kachikwu, Inji shugaban VON

Buhari zaiyi sulhu tsakanin Baru da Kachikwu, Inji shugaban VON

Ya cigaba da bayyani cewa duk da shi yana garin Enugu ne kuma bai samu ganawa da shugaba Buhari ba, yana lura da nazirin abubuwan da ke kaiwa su komo a fadar shugaban kasar, hakan ne ma yasa yake ganin wadanda suke hana Kachikwu ganin shugaba Buhari ne suka hana wasikar ta isa hannun shugaban kasan.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa Biyafara ba zata taba gushewa ba, Inji Ikedife

Da yake amsa tambayar cewa ko Shugaban Kasan ne ke gudanar da harkokin mulkin kasar, ya amsa da cewa shugaba Buhari ba mutum bane mai son magana da yawa, baya garaje ko sauri cikin aikin sa wadda hakan ne ke haifar da nasara. Yayi kira da mutane suyi watsi da farfaganda irin ta su gwamna Fayose na jihar Ekiti da sauran yan jam'iyyar PDP.

Ya bada misalin nasarori da shugaba Buhari ya samu a fanoni daban-daban kamar yaki da Boko Haram, Yaki da cin hanci da rashawa, ginin layin dogo, da kuma sauran ayyukan cigaban kasa, duk wannan alamu ne cewa shugaba Buharin shi ke jan ragamar mulkin kasar ba yan fada ba.

Daga karshe yace Shugaba Buhari mutum ne mai sauraron jama'a kuma ba zai bari wani mahaluki guda ya bata masa aikin sa ba, saboda haka duk wanda aka samu da laifi za'a iya sallamarsa tunda aikin daukar sa aikin akayi na wani lokaci.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel