Allah ya yiwa mataimakin shugaban APC a Zamfara rasuwa

Allah ya yiwa mataimakin shugaban APC a Zamfara rasuwa

- Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara, Alhaji Lawali Bala Yabacaco ya rasu

- Marigayin ya mutu yana da shekaru 52 da haihuwa.

- An binne shi a Gusau bisa ga tsarin addinin Musulunci

Allah ya yiwa mataimakin shugaban jam'iyyar mai mulki ta APC na jihar Zamfara, Alhaji Lawali Bala Yabacaco rasuwa.

Marigayin ya mutu yana da shekaru 52 da haihuwa.

Alhaji Lawali ya mutu a yau Lahadi, 8 ga watan Oktoba a wani asibiti mai zaman kanta da ke Gusau, babban birnin jihar bayan gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin ya bar mata 3 da yara 20 da kuma jikoki 2. An riga an binne shi a Gusau bisa ga tsarin addinin Musulunci.

KU KARANTA: Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

"Yana fama da rashin lafiya a wasu lokuta ko da yake rashin lafiyar ba mai tsanani ba ne. Mun yi mamakin mutuwar marigayin wanda masani ne a fanin siyasar kuma mai hankali", kamar yadda kakakin APC a jihar, Alhaji Ibrahim Gidan Tsaka ya shaidawa majiyar NAIJ.com.

Bisa ga rahotanni wani jigon dan jam'iyyar APC a jihar, Alhaji Bello Imam shi ma ya rasu bayan wata rashin lafiya.

An kuma binne shi a Gusau babban birnin jihar. Jana'izar ta samu halarcin mataimakin gwamna, Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad da sauran jami'an gwamnati da magoya bayan jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel