Babu tsoron Allah a gina cocina a ko ina – Kadinal Okogie

Babu tsoron Allah a gina cocina a ko ina – Kadinal Okogie

- Kadinal Okogie ya caccaki shugaban cocin RCCG Fasto Enoch Adeboye akan gina cocina a ko ina

- Okogie ya ce Adeboye ya mayar da al'amarin addini kasuwanci a Najeriya

- Shugaban cocin katolika ya ce yawan cocina a kasar ya sa yan Najeriya sun rage tsoron Allah

Shugaban cocin darikar Katolika na jihar Legas, Kadinal Anthony Olubunmi Okogie, ya caccaki shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye akan yunkurin kara gina cocina a ko ina a fadin kasar.

Okogie ya kalubalanci yunkurin Adeboye na gina cocina a ko ina a fadin kasar da cewa, ya mayar da al’amarin addini kasuwanci saboda gina cocina a ko ina bashi bane tsoron Allah.

Kadinal Okogie yace yawan cocina a kasar nan, ya sa yan Najeriya sun rage tsoron Allah.

Babu tsoron Allah a gina cocina a ko ina – Kadinal Okogie

Babu tsoron Allah a gina cocina a ko ina – Kadinal Okogie

A wata zantawa da yayi da yan Jaridar Telegraph, Okojie ya ce: “Tsoron Allah shine abun na farko da zai kawo hadin kan al’ummar kasar nan. Yan Najeriya a yanzu ba su da tsoron Allah.

KU KARANTA : El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019

Yadda Adeboye yace zai gina cocina a ko ina a fadin kasar nan, idan Musulmai suma suka ce za su gina massalatai a ko ina, hakan ya nuna yan Najeriya basa tsoron Allah.

“Kullun muna ji labarin kashe kashe a wurari da ba mu taba jin anyi kisa ba.

“Rashin tsoron Allah ya sa al'ummar kasar nan ba sa cikin natsuwa. Mutum ba zai iya yawo cikin kwanciyan hankali ba saboda fargaban kada wani abu ya faru da shi.

“A mayar da al’amarin addini kasuwanci a Najeriya,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel