Sojoji sun yi wa wasu 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe biyu

Sojoji sun yi wa wasu 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe biyu

- Har yanzu dai ana nan ana batakashi tsakanin sojojin Najeriya da 'yan Boko Haram

- Ofereshon Lafiya Dole ta kar biyu daga cikin gunun da suke neman shiga dajin Sambisa

- An gan su dauke da kayan abinci

Kungiyar sojojin Najeriya ta ce a jiya ne kungiyar ta ta Ofereshon Lafiya Dole ta kashe 'yan Boko Haram biyu a kauyen Mayanti, a karamar hukumar Bama, dake jihar Borno. Mai magana da yawun bakin sojojin ne, Kingsley Samuel, ya fadi haka.

Sojoji sun yi wa wasu 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe biyu

Sojoji sun yi wa wasu 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe biyu

Ya ce an yi wa gungun 'yan Boko Haram din kwanton bauna ne a yayin da aka gansu suna kokarin shigewa cikin dajin Sambisa da kayan abinci.

"Mun kashe mutum biyu, mun raunata wasu, sauran kuma sun yi watsi da abin suke dauke da shi sun ranta a na kare.

DUBA WANNAN: Kamfanin wutar lantarkin Inugu ya sha alwashin kamo masu satar layi

"Wannan ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata da misalin karfe 10: 45 na dare. Mun samu buhunhuna masara a wajen bayan da 'yan Boko Haram din suka arce."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel