Gawar tsohon shugaban NANS ya isa Najeriya daga Indiya

Gawar tsohon shugaban NANS ya isa Najeriya daga Indiya

- Gawar tsohon shugaban kungiyar dalibai na kasa, NANS, Dauda Mohammed ya iso Najeriya

- Allah ya yiwa Muhammed cikawa a ranar Lahadi da ta gabata a kasar Indiya

- Mohammed ya kasance shugaban NANS daga 2011 zuwa 2012

An iso da gawar tsohon shugaban kungiyar dalibai na kasa, NANS, Dauda Mohammed, mai shekaru 38 haihuwa daga Indiya.

Allah ya yi masa cikawa a ranar Lahadi da ta gabata a kasar Indiya inda ya tafi neman magani, amma aka sanar da rasuwarsa minti biyar kafin ya sauka a filin jirgin saman Delhi.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Mista Mohammed ya bar birnin Abuja zuwa kasar Indiya a ranar 30 ga watan Satumba don neman maganin ciwon hanta da yake fama da ita.

Gawar tsohon shugaban NANS ya isa Najeriya daga Indiya

Gawar tsohon shugaban NANS, Dauda Mohammed

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun fasa Neja-Delta da Operation crocodile smile II

An haife shi a shekarar 1979, Mista Mohammed wanda shi ne shugaban NANS daga 2011 zuwa 2012, ya halarci jami'ar Jos.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel