An kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu saboda bashin Naira N7,500

An kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu saboda bashin Naira N7,500

- Bashi ya janyo an kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu

- Yan Najeriya sama 116 aka kashe a kasar Afrika ta kudu a cikin wannan shekara

- Mai laifin ya shiga hannun hukumar yansandar kasar Arika ta kudu

An harbe wani dan Najeriya har lahira a kasa Afrika ta kudu saboda zargin bashin Rand 300 (N7,500).

Shugaban kungiyar yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, Adetola Olubajo, ya fa da ma yan jarida cewa “ Al’amarin ya faru ne a yayin da mamacin da aka harbe mai suna Jelili Omoyele mai shekaru 36 yake takaddama da wani dan kasar akan bashin Rand 300 wanda yayi dadai da N7,500 kudin Najeriya.

An kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu saboda bashin Naira N7,500

An kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu saboda bashin Naira N7,500

“Yansandar garin Jeppes town sun kama mai laifin.

KU KARANTA : Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

Wannan mumunar al’amari ya faru ne mako daya bayan an kashe wani dan Najeriya a wata unguwa dake kusa da baban birnin tarayya kasar Johannesburg.

Mai ba shugaban kasa shawara a fannin harkokin kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ta ce an kashe yan Najeriya sama da mutane 116 a kasar Afrika ta kudu a cikin wannan shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel