Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

- Zanga-zangar dalibai wacce ta biyo bayan mutuwar wasu abokan su guda biyu a asibitin makarantar

- Dalibai biyu sun mutu a asibitin makarantar bayan kamuwa da zazzabin cizon sauro

- Daliban na zan-zangar nuna fushin su da rashin samar da kayayyakin walwalar dalibai daga bangaren shugabancin makarantar

A yau lahadi ne rijistaran faltaknik mallakin gwamnatin tarayya dake Ado Ekiti ya sanar da rufe makarantar na din-din-din biyo bayan barkewar wata zanga-zangar dalibai wacce ta biyo bayan mutuwar wasu abokan su guda biyu a asibitin makarantar ranar juma'a.

Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

Zanga-zangar mutuwar dalibai biyu ta jawo rufe makarantar faltaknik a jihar Ekiti

Rikici ya barke a makarantar ne tun ranar juma'a bayan da wasu dalibai biyu da suka kamu da zazzabin cizon sauro kuma aka garzaya dasu asibitin makarantar inda suka ce ga garinku nan jiya asabar. Bayan samun labarin mutuwar daliban, sai abokan su sukayi gangami suka nufi asibitin a fusace, kuma da zuwan su suka fara lalata kayayyaki kafin daga bisani su fito su datse hanyar zuwa makarantar, dalilin da ya haddasa cunkoson ababen hawa a titin makarantar.

DUBA WANNAN: Kungiya ta shigar da gwamnatin tarayya kara a kan cigaba da biyan tsofin gwamnoni albashi a matsayin sanatoci da ministoci

Daliban na zan-zangar nuna fushin su da rashin samar da kayayyakin walwalar dalibai daga bangaren shugabancin makarantar, kamar yadda wani dalibi da bai yarda a bayyana sunan sa ba ya shaida.

Dalibin ya ce babu wani magani a asibitin makarantar bayan farasitamol kuma shine magani kadai da aka bawa daliban maimakon yi masu allurar maganin zazzabin cizon sauro lokacin da aka kai su asibitin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel